Isa ga babban shafi

'Yan awaren Polisario sun katse hulda da Spain

Kungiyar ‘yan awaren Polisario, mai fafutukar neman 'yancin kai na yankin yammacin Sahara, ta sanar da  yanke hulda da Spain, bayan da kasar ta goyi bayan shirin gwamnatin Morocco na bai wa yammacin Saharar kwarya-kwaryar ‘yancin kai.

Sojojin yankin Polisario na Morocco yayin fareti
Sojojin yankin Polisario na Morocco yayin fareti FAROUK BATICHE/AFP via Getty Images
Talla

Kasar Spain ta goyi bayan shirin cin gashin kansa a matsayin wata hanya ta warware takaddamar da ta dade tana fama da ita a yankin yammacin Sahara, wanda Maroko ke daukarsa a matsayin yankinta.

Sai dai kungiyar Polisario da ke samun goyon bayan Algeria ta yi watsi da shawarar, inda ta zabi a kada kuri'ar raba gardama kan samun 'yancin kan kafa kasa mai zaman kanta.

Har yanzu dai babu kwakkwarar dangantaka tsakanin Morocco da Spain tun bayan da kasar ta Spain ta baiwa shugaban mayakan Polisario Brahim Ghali damar shiga cikinta domin jinya a watan Afrilun bara, ba tare da fadawa Moroccon a hukumance ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.