Isa ga babban shafi

Mutane miliyan 18 na fuskantar matsalar rashin abinci a yankin Sahel

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa kimanin mutane miliyan 18 a yankin Sahel na fuskantar matsalar karancin abinci, a dai dai lokacin da wanda aka bayar a matsayin tallafi ke shirin karewa, gami da fuskantar karancin kudaden dorewar shirin tallafin.

Wasu 'yan kasar Senegal dake yankin Matam a arewa maso gabashin kasar.
Wasu 'yan kasar Senegal dake yankin Matam a arewa maso gabashin kasar. AP - Rebecca Blackwell
Talla

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP ta ce rikice-rikice, da annobar COVID-19, da sauyin yanayi da kuma hauhawar farashin kayayyaki ne ke kara jefa miliyoyin mutane a yankin kudu da Saharar Afirka cikin halin kaka ni kayi.

WFP ta ce tuni ta rage adadin tallafin abinci a wasu yankunan da abin ya shafa, yayin da ake fuskantar raguwar himmar masu bayar da agaji na kasa da kasa.

A farkon watan Afrilu, kungiyoyin bada agaji na duniya suka yi alkawarin taimakawa kasashen Sahel da wadanda ke kewaye da Tafkin Chadi da kudin da ya kai kusan Dala biliyan 2 domin shawo kan yunwar da ta addabi yankunan biyu.

Kasashen da ake saran su ci gajiyar taimakon sun hada da Burkina Faso da Kamaru da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar da kuma Najeriya wadanda tashe tashen hankula da kuma karancin ruwan sama suka hana aikin noma da samar da abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.