Isa ga babban shafi

Yankunan Sahel da Tafkin Chadi za su samu tallafin euro biliyan 2 kan yunwa

Kungiyoyin bada agaji na duniya sun yi alkawarin taimakawa kasashen Sahel da wadanda ke kewaye da Tafkin Chadi da kudin da ya kai kusan Dala biliyan 2 domin shawo kan yunwar da ta addabi yankunan biyu.

Wata mata dauke da ruwa a sansanin 'yan gudun hijira a garin Ouallam, Nijar, 6 ga Yuli, 2021.
Wata mata dauke da ruwa a sansanin 'yan gudun hijira a garin Ouallam, Nijar, 6 ga Yuli, 2021. © REUTERS/Media Coulibaly/File Photo
Talla

Gidauniyar da Majalisar Dinkin Duniya ta kaddamar ya nuna cewar kungiyar kasashen Turai ta EU zata bada gudumawar euro miliyan 240, bayan wasu euro miliyan 654 da tace ta ware domin bunkasa yankin, sai kuma kasar Faransa da tayi alkawarin bada euro miliyan 166 na abinci a cikin wannan shekara.

Kasashen da ake saran su ci gajiyar taimakon sun hada da Burkina Faso da Kamaru da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar da kuma Najeriya wadanda tashe tashen hankula da kuma karancin ruwan sama suka hana aikin noma da samar da abinci.

Hukumar samar da abinci ta Majalisar Dinkin Duniya tace matsalar karancin abincin da ake fama da ita a yankin a shekarar 2019 ya ribanya har sau 4 inda ta shafi mutane sama da miliyan 40 sabanin miliyan kusan 11 da ake da shi shekaru 3 da suka gabata.

Wadannan alkawura sun biyo bayan taron da wata kungiya da ake kira ta Sahel da Afirka ta Yamma ta shirya da taimakon kungiyar kasashen Turai da kuma kungiyar yaki da karancin abinci ta duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.