Isa ga babban shafi

Kasashen Gabashin Afirka na shirin kafa rundunar yankin saboda tsaro

Manyan hafsoshin sojin kasashen gabashin Afrika sunyi wata ganawa ranar Talata da nufin kafa wata rundunar musamman da zata tun kari kalubalen tsaron da ake fuskanta a yankin gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango.

Wasu sojojin Jamhuriyar Demokradiyar Kwango
Wasu sojojin Jamhuriyar Demokradiyar Kwango © AFP/Guerchom Ndebo
Talla

Ganawar data gudana a garin Goma ta maida hankali ne kan lalubo hanyoyin daza’abi wajen magance rikicin daya jima yana addabar Gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango, wadda ta zamo mamba a kungiyar kasashen yankin cikin watan Maris.

Acewar manyan hafsoshin sojin, kafa wannan runduna shine hanyar kawo karshen zubda jinin da ake a gabashin na Kwango.

Jamhuriyar Demokradiyyar Kwangon dai ta yi iyaka ne da kasashen Ruwanda da Burundi da Uganda, inda hukumomin ke zargin Ruwanda da marawa kungiyoyi masu dauke da makamai baya, wajen cin karen su babu babbaka a yankunan ta, cikin su harda kafuwar kungiyar mayakan M23 wanda suka gwabza fada da dakarun gwamnati baya bayan nan.

Dubban mutane ne dai suka rasa rayukan su da  muhallan su a rikice rikice daban daban a yankin gabashin Kwango.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.