Isa ga babban shafi

Rwanda da Congo na tattaunawa a Angola don dinke barakar da ke tsakaninsu

Shugaban Rwanda Paul Kagame da takwaransa na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo Felix Tshisekedi na wata tattaunawa yanzu haka a birnin Luanda na Angola a wani yunkuri na warware tsamin dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu makwabtan juna.

Shugaba Paul Kagame na Rwanda da takwaransa Félix Tshisekedi na DR Congo.
Shugaba Paul Kagame na Rwanda da takwaransa Félix Tshisekedi na DR Congo. AFP - SIMON WOHLFAHRT
Talla

Kasashen biyu duk sun tabbatar da isar shugabannin su Luanda babban birnin kasar Angola dake gabar tekun kudancin Afirka, domin amsa gayyatar shugaba Jawo Lurenco dake shiga tsakani domin kwantar da hankular takwarorinsa dake tada jijiyoyin wuya.

Cikin wata sanarwa ofishin shugaban jamhuriyar demokradiyar Congo Felix Tchisekedi yace wannan itace ganawar farko da zaiyi da takwaransa na Rwanda Paul Kagame tun bayan kazancewar hare-haren mayan M23 a gabashin congo.

Shugaban kasar Angola Joao Lourenco, wanda kungiyar tarayyar Afirka ta nada amatsayin babban mai shiga tsakanin kasashen dake yankin Tafkin Congo, da dangantaka ta yi tsami tsakaninsu, sakamakon zargin da Kinshasa ke yi wa Kigali na taimawa ‘Yan tawayen M23.

Kasar Rwanda ta sha musanta goyon bayan 'yan tawayen, yayin da kasashen biyu ke zargin juna da kai hare-hare a kan iyakokisu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.