Isa ga babban shafi

Jamhuriyar Congo ta rufe iyakarta da Rwanda

Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo ta rufe iyakarta da Rwanda, biyo bayan bindige wani sojanta da aka yi, a lokacin da ya kai hari kan wasu jami’an tsaro a cikin iyakar kasar ta Rwanda.

Kan iyakar Jamhuriyar Congo da kasar Rwanda.
Kan iyakar Jamhuriyar Congo da kasar Rwanda. REUTERS/Djaffer Sabiti
Talla

Matakin rufe kan iyakar dai shi ne na baya bayan dake dada rura wutar rikicin diflomasiyya tsakanin kasashen biyu masu mawaftaka da juna, tun bayan da ‘yan tawayen M23 da gwamnatin Jamhuriyar Congo ke zargin Rwanda na taimaka musu, suka kaddamar da jerin hare hare a gabashin kasar a watan Mayun da ya gabata.

Rwanda na cigaba da musanta zargin da ake mata na marawa mayakan M23 baya, wadanda tushensu ya fito daga kabilar Tutsi, ta shugaban Rwanda mai ci Paul Kagame, da kuma tuhumar cewa Rwandan ce ta tura mayakan zuwa gabashin Congo.

Akalla ‘yan sandan Rwanda 2 ne suka jikkata a lokacin da sojan Congo ya tsallaka iyaka tare da bude musu wuta, kafin daga bisani wani sojan kasar ta Rwanda ya harbe shi har lahira.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.