Isa ga babban shafi

Sabon fada ya barke tsakanin sojojin Demokradiyar Congo da 'Yan tawayen M23

An sake gwabza kazamin fada a Jamhuriyar Demokradiyar Congo ranar Lahadi, bayan da 'yan tawayen M23 suka sake kai wani sabon hari kan sojoji a garin Bunagana da ke gabashin kasar.

Wasu 'yan tawaye a Gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Congo.
Wasu 'yan tawaye a Gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Congo. © ©Facebook
Talla

Damien Sebusanane, shugaban wata kungiyar farar hula na yankin ya ce galibin al'umma sun tsere daga tsakiyar Bunagana, dake zama muhimmiyar hanyar jigilar kayayyaki a kan iyakar kasar da Uganda.

Zargin Rwanda

An sake samun barkewar fada tsakanin sojoji da 'yan tawayen M23 a yankin, wanda gwamnatin kasar ta dora alhaki kan makwabciyarta Rwanda. Sai dai Rwanda ta sha musanta goyon bayan kungiyar 'yan tawayen.

An kai wa sojojin hari ne da safiyar Lahadi a Bunagana da kuma garin Tshengerero da ke kusa, dukkansu a lardin Kivu ta Arewa, in ji wani jami'in soji na yankin Kanar Muhindi Lwanzo.

Kawanya

Sebusanane ya ce mayakan na M23 sun yi wa Bunagana kawanya, kuma tankokin sojin Congo suna ta luguden wuta a kan 'yan tawayen daga cikin garin.

Wani jami’in sojan da ya ki bayyana sunansa ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa, sojojin kasar Congo suna fatattakar ‘yan tawayen, inda ake ci gaba da gwabza fada a kan hanyar Bunagana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.