Isa ga babban shafi

M23 ta yi watsi da kiran shugabannin Rwanda da Congo kan tsagaita wuta

Kungiyar M23 ta yi watsi da tattaunawar shugabannin Rwanda da na Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo, wadda ta kai ga cimma jituwa don tabbatar da zaman lafiya a tsakanin kasashen biyu makwabtan juna, biyo bayan rikicin baya-bayan nan saboda hare-haren kungiyar.

Mayakan M23 da ke hare-hare a gabashin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo.
Mayakan M23 da ke hare-hare a gabashin Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo. AFP - GUERCHOM NDEBO
Talla

Yayin ganawar ta shugaba Paul Kagame na Rwanda da takwaransa Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Congo jiya laraba a birnin Luanda na Angola shugabannin biyu sun amince da kawo karshen rikicin da ke tsakaninsu ciki har da hare-haren na M23 da Congo ke zargin Rwanda da daukar nauyi.

Sai dai sanarwar da kungiyar ta fitar yau Alhamis ta ce shugabannin biyu sun yi kadan su iya kawo karshen rikicin na gabashin Jamhuriyyar Congo.

A ganawar shugabannin biyu dai sun bukaci gaggauta sakin wadanda ake tsare da su tare da janyewar mayakan na M23 daga yankin da suke yanzu haka a Jamhuriyar Congo ba kuma tare da wasu sharudda ba.

Sai dai kakakin kungiyar ta M23 Major Willy Ngoma ya shaidawa kafofin labarai cewa baza su bar inda su ke a gabashin Congon ba, domin kuwa a cewarsa su cikakkun ‘yan kasa ne, babu dalilin da zai sanya su barin kasarsu.

A cewar Major Ngoma, rikicin matsalar siyasa ce tsakanin ‘yan Congo kuma su ya kamata su zauna teburi don sulhunta kansu.

Kungiyar ta M23 mai rike da makami a gabashin Congo ta jima ta na ikirarin cewa ta na yakin ne don neman ‘yanci da kuma baiwa yankin kariya daga wariyar da ya ke fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.