Isa ga babban shafi

Mutane fiye da dubu 1 da 400 na halarta taron sasanta rikicin kasar Chadi

Yau an bude gagarumin taron sasanta rikicin siyasar kasar Chadi da gwamnatin Soji ta shirya, wanda ke dauke da mahalarta sama da 1,400 daga bangarorin siyasar kasar da dama da kuma yan tawayen da suka aje makaman su da kungiyoyin faraen hula da kuma shugabannin kungiyoyin kwadago.

Taron sasanta rikicin kasar Chadi a birnin N'Djamena.
Taron sasanta rikicin kasar Chadi a birnin N'Djamena. © Christophe Petit Tesson/AFP
Talla

Yayin bude taron, shugaban kasa Janar Mahamat Idris Deby wanda ya bayyana taron a matsayin shirin sa na kawo karshen matsalolin siyasar da suka addabi kasar, ya bayyana taron a matsayin na yanke hukunci akan makomar kasar domin shata makoma.

Shugaban ya ce taron zai bude kofar yanci da kuma zaben dimokiradiya bayan kwashe watanni 18 na mulkin sojin kamar yadda kasar Faransa da kungiyar kasashen Afirka ta AU ta bukace shi ya mutunta domin mayar da mulki ga fararen hula.

Kafin bude taron sanda shugaba Deby ya kaddamar da wani mutum mutumi dake nuna alamar hadin kan kasa a Dandalin ‘Yanci da ake yiwa lakabi da ‘January 15’ dake Birnin Ndjamena, inda ya karbi faretin soji.

Akalla kungiyoyi 40 suka rattaba hannun halartar taron na Ndjamena, bayan wanda ya gudana a Doha, duk da janyewar da wasu suka yi, cikin su harda kungiyar FACT wadda tace sojojin sun shirya taron yadda zai amince da bukatun su.

Ita ma kungiyar Wakita Tama da ta hada da tarin jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula na kauracewa taron saboda zargin da take yiwa gwamnati na take hakkin Bil Adama.

Wasu masu adawa da taron na zargin cewar shugaban sojin mahamat Deby na shirin tsayawa takarar shugaban kasa.

Success Masra, shugaban Jam’iyar ‘Transformers’ da ke cikin kawancen Wakit Tamma ya bukaci gudanar da bore a wajen bude taron.

Bayan bikin bude taron, a ranar litinin mai zuwa ake saran taron ya kankama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.