Isa ga babban shafi

Matasan Congo sun amsa kiran shugaba Tshisekedi na kare kasarsu daga M23

A Jamhuriyar Demokradiyar Congo, da alama kiran da shugaban kasar Felix Tshisekedi ya yi wa matasan kasar da su tashi tsaya don kare kasar daga ‘yan tawayen M23 ya samu karbuwa, inda daruruwan matasan kasar suka amsa kiran tare da mika kai.

Wasu matasan jamhuriyar Congo
Wasu matasan jamhuriyar Congo © twitter
Talla

Daraktan kula da daukar ma'aikata na rundunar sojin kasar a lardin arewacin Kivu Ndakala Faustin, yace "Tun daga safiyar Asabar kimanin matasa Maza da Mata 800 suka bukaci shiga aikin na sakai.

Ranar Jumma’a ne Shugaban Felix Tshisekedi ya bukaci goyon bayan matasan kasar a kokarin da jami’an tsaro ke yi na yakar ‘yan tawayen kungiyar M23 da zuwa yanzu suka kwace iko da wasu sassa na kasar.

Nauyin kare kasa

Shisekedi ya bayyana cewa nauyi ne dake kan matasan yankunan da barazanar ta M23 ta fi tsananta kan su zama mayakan sa kai don taimakawa jami’an tsaron wajen yakar ‘yan tawayen wadanda ke kokarin raba su da matsugunansu.

Daga ranar 20 ga watan Oktoban da ya gabata zuwa yanzu mutanen da yawansu ya haura dubu 183 ne suka tserewa hare-haren M23 daga arewacin Kivu tare da tattaruwa a sansanin wadanda suka rasa matsugunansu na Kanyarucyinya na kasar ta Congo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.