Isa ga babban shafi

Sojin Congo sun yiwa sansanin mayakan M23 luguden wuta da jiragen yaki

Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo ta yi amfani da sabbin jiragen yakin da ta saya a kwanakin nan, wajen yiwa sansanin mayakan tawayen M23 ruwan wuta, abinda ya tilastawa mayakan da suka tsira tsallakawa makwaftan kauyuka don tsira da rayukan su.

Mayakan M23 a Congo.
Mayakan M23 a Congo. AFP - GUERCHOM NDEBO
Talla

Kungiyar ta M23 da ke da mambobi mafi yawan su ‘yan kanilar Tutsi sun fara bulla a kasar a 2012, yayin da suka sake dawowa da karfin su a 2021, inda kuma a hankali suka fara kame yankunan birnin Goma mafi girma a Gabashin kasar, kafin a fatattake su.

Mayakan dai sun sake daukar makamai ne bayan da suka zargi gwamnatin kasar da gaza cika alkawurran da ta dauka a yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma da juna musamman sanya su cikin dakarun sojin kasar da sauran Bukatu.

Tun bayan sake bullar tasu sun yi nasarori da dama a kan sojojin kasar musamman a arewacin Kivu, yayin da suke ci gaba da karbe iko da garuruwan da ke gab da yankin.

Sake bullar ta su dai ya haifar da rashin fahimta tsakanin Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo da Rwanda, bayan da Congon ta zargi Rwanda da marawa M23 din baya da kuma karfafa musu gwiwa.

Sai dai kuma a Talatar nan ne sojojin kasar suka sanar da gagarumar Nasarar tarwatsa manyan sansanonin M23 din a kauyen Tchanzu dake arewacin Kivu, tare da bada tabbacin ci gaba da luguden wutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.