Isa ga babban shafi

M23 ta fara garkuwa da Matasa a Congo don hanasu shiga aikin sa kai

Wasu rahotanni daga Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo na cewa ‘yan tawayen M23 sun fito da wani salon kame dukkanin majiya karfi a arewacin kasar don dakile mayakan sa kai da suka yi dafifi wajen taimakon dakarun gwamnati da yakin da ta ke da ‘yan tawayen.

Matakin 'yan tawayen na M23 na da nasaba da yadda Matasa ke ci gaba da tururuwa don shiga aikin sa kai da nufin yakarsu.
Matakin 'yan tawayen na M23 na da nasaba da yadda Matasa ke ci gaba da tururuwa don shiga aikin sa kai da nufin yakarsu. AFP - GLODY MURHABAZI
Talla

A karshen makon jiya ne fada ya sake dawowa sabo tsakanin ‘yan tawayen na M23 inda mayakan suka kaddamar da hare-hare a Goma da ke arewacin lardin Kivi tare da kame tarin matasa majiya karfi bisa zarginsuu da kasancewa sojojin sa kai.

Kungiyar ta M23 wadda Amurka da Majalisar Dinkin Duniya ke zargi da samun goyon baya daga Rwanda wadda kuma galibin mayakanta ‘yan kabilar Tutsi ne ta farmaki kauyukan Bishusha da Tongo ko da ya ke babu bayan ikan adadin mutanen da mutu a gwabzawar.

Wani mazauni garin da ‘yan tawayen na M23 suka farmaka ya bayyana yadda mayakan sa kai da ke bayar da tsaro ga garuruwan suka gwabza yaki tsakaninsu da ‘yan tawayen da suka farmaki yankin nasu.

Majiyar Sojin kasar ta Congo ta bayyana cewa tuni dakarun Soji suka isa yankin don ci gaba da gwabza fada da ‘yan tawayen.

Akalla matasa 50 majiya karfi ‘yan tawayen na M23 suka yi garkuwa da su a garin Tonga wadanda galibinsu mambobin mayakan sa kai ne na kungiyar FDLR ta ‘yan kabilar Hutu da ke da daddiyar gaba da ‘yan kabilar ta Tutsi.

Iyalan wadanda aka yi garkuwar da su, sun bayyana cewa ‘yan tawayen na M23 sun saki mata 15 da ke cikin yayinda Mazan kuma aka boye su a kauyen Rutshuru.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.