Isa ga babban shafi

An rufe makarantu a Malawi saboda annobar amai da gudawa

Hukumomi a Malawi sun sanar da matakin rufe makarantu har sai lokacin da hali yayi, bayan barkewar annobar amai da gudawa a biranen kasar da dama.

yadda ake bawa marasa lafiya kulawar gaggawa a cibiyar kula da masu cutar Kwalara a kasar Haiti kenan.
yadda ake bawa marasa lafiya kulawar gaggawa a cibiyar kula da masu cutar Kwalara a kasar Haiti kenan. AFP - RICHARD PIERRIN
Talla

Rahotanni daga kasar na cewa ana sa ran dalibai za su koma karatu a ranar Talatar nan bayan hutun bukukuwan Kirismeti da na sabuwar shekara.

Sai dai ma’aikatar lafiya ta kasar ta ce za a dakatar da karatun dalibai a kasar, musamman Lilongwe babban birnin kasar ,da kuma kudancin Blantyre da za a dakatar har tsawon makonni buyi.

Ministan lafiya na Malawi Khumbize Chiponda a wata sanarwa da ya fitar, ya ce dakatar da dalibai zuwa karatu na da nasaba ne da kamarin cutar da ke kara yaduwa a sassan kasar, yayin da ake samun karuwar wadanda cutar take kashewa.

Kasar da ke kudancin Afirka mai fama da talauci ta samu kusan mutane 18,000 da suka kamu da cutar inda mutane 595 suka mutu tun daga watan Maris, abin da Majalisar Dinkin Duniya ta ce ita ce annoba mafi girma da kwalara ta haifar a cikin shekaru 10 da suka gabata.

A watan Satumba, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta yi gargadin cewa, duniya na iya fuskantar annobar cutar kwalara, sakamakon kalubalen da sauyin yanayi ke ci gaba da haifarwa ga duniya.

WHO ta ce, cutar na shafar mutane tsakanin miliyan 1.3 zuwa miliyan hudu a kowace shekara a fadin duniya, tare da asarar rayukan mutum 143,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.