Isa ga babban shafi

Bam ya tashi a wani coci a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo

Rundunar sojin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo ta ce wani abu mai fashewa ya tashi a cikin wata mujami’a a lardin arewacin Kivu, sai dai ba ta  bada Karin bayani a kan adadin wadanda suka jikkata ba.

Taswirar da ke nuna yaankin Kivu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo.
Taswirar da ke nuna yaankin Kivu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo. RFI
Talla

A wata sanarwa da ya aike wa manema labarai, kakakin rundunar sojin, Anthony Mualushayi  ya ce harin ta’addancin ya auku ne  a wani cocin pentacostal  da ke garin Kasindi a arewavin Kivu, wanda ke kusa d iyakar kasar da Uganda.

Mualushayi ya ce jaami’an tsaro sun riga sun karbe iko da inda lamarin ya auku, kuma tuni aka kai wadanda suka ji rauni asibiti, yana mai za a  gudanar da bincike.

Har yanzu dai babu wai cikakken bayani a game da wannan lamari, musammamn ma adadin wadanda suka jikkata, da kuma wadanda suka kai harin.

Kimanin kungiyoyin ‘yaan tsagera masu daukie da makamai guda 120 ne ke yin abin da suka ga dama a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo mai arzikin albarkatun kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.