Isa ga babban shafi

Kamaru na shirin rage farashin kalanzir da gas na girki bayan janye tallafin mai

Al’umma a Kamaru sun fara shiga rudani yayin da sabon farashin ya fara aiki a wannan Laraba 01 ga watan Fabarairu bayan da gwamnatin kasar ta sanar da janye tallafin da take sanyawa a farashin man fetur, matakin da ya kaiga tashin farashin man teur da kashi 15 bisa 100, saboda matsin lamba daga asusun bada lamuni na duniya IMF.

Gwamnatin kasar Kamaru ta sanar da janye tallafin da take sanyawa a farashin man fetur saboda matsin lamba daga asusun bada lamuni na duniya IMF.
Gwamnatin kasar Kamaru ta sanar da janye tallafin da take sanyawa a farashin man fetur saboda matsin lamba daga asusun bada lamuni na duniya IMF. AP - Frank Augstein
Talla

A karkashin sabon farashin, za’a rika sayar da litar mai akan Cefa 730 maimakon Cefa 630 da ake sayar da man a baya.

Tun ranar 31 ga watan Disambar a zawabin shugaban kasar Paul Biya na jajiberen sabuwar shekara ya sanar da shirin janye tallafi da ake sanyawa a fannin man fetur.

Sabon matakin yasa farashin man fetur da dizal a fanfuna ya tashi da kashi 15.4% da kuma 25.2%, yayin da man da ake sayar wa masana'antu za a kayyade kan CFA 560.19 kowace lita.

Karin albashin ma'aikata

Sanarwar da gwamnatin ta fitar ta ce zata dauki matakai da dama na daidaita al’amura don ganin matakin bai shafi al’umma ba sosai, ciki harda shirin ƙarin kashi 5.2% na albashin ma'aikatan tare da rage farashin kalanzir da gas na girki.

Gwamnatin ta kuma ce za ta fara tattaunawa kan karin mafi karancin albashi.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.