Isa ga babban shafi

MDD tace mutane 171 M23 ta kashe a Jamhuriyar Demokradiyar Congo cikin wata daya

Majalisar Dinkin Duniya tace akalla fararen hula 171 'Yan tawayen M23 suka kashe a gabashin Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango a watan Nuwambar data gabata, sabanin adadin 131 da data bayyana a baya. 

'Yan tawayen M23 a wani yankin Gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Congo.
'Yan tawayen M23 a wani yankin Gabashin Jamhuriyar Demokradiyar Congo. REUTERS - JAMES AKENA
Talla

A cikin wata takarda da ta fitar da ke nuna irin cin zarafin da aka yi a kasar a shekarar da ta gabata, ofishin hadin gwiwa na Majalisar Dinkin Duniya da hukumar kare hakkin bil adama, ya ce kungiyar M23 ta kashe akalla fararen hula 171 a yankunan Kishishe da Bambo da ke gabashin lardin Kivu ta Arewa. 

Kisan kiyashin ya janyo bacin rai a kasar, inda 'yan kabilar Tutsi na M23 suka kwace yankuna da dama a arewacin Kivu tun daga karshen shekara ta 2021 tare da raba dubban daruruwan mutane da muhallansu.

Binciken farko da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar ta bayyana cewa an kashe fararen hula 131. 

Dama dai Alkaluman da aka ruwaito na girman kisan kiyashin sun bambanta sosai, inda gwamnatin kasar ta ce an kashe kimanin mutane 300, yayin da kungiyar M23 ta ce an harbe fararen hula takwas. 

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta bayyana cewa kungiyar ta M23 ta kashe akalla mutane 22 a Kishishe  

A cikin sanarwar ta ranar Talata, Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta yi rikodin take hakkin bil adama kusan 6,000 a kasar a bara - wanda ke nuna  raguwar kashi 15 cikin 100 idan aka kwatanta da 2021. 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.