Isa ga babban shafi

An harbe har lahiraShahararren mawakin nan Kiernan Forbes dan Afika ta kudu

An harbe daya daga cikin fitattun mawakan rap na Afirka ta Kudu, Kiernan Forbes, wanda aka fi sani da AKA, a wajen wani gidan cin abinci a birnin Durban na kudu maso gabashin kasar, kamar yadda iyalansa suka fada a yau asabar.

Birnin Durban, na Afrika ta kudu
Birnin Durban, na Afrika ta kudu AFP PHOTO / GIANLUIGI GUERCIA
Talla

Dan shekaru 35 ya lashe kyaututtuka da dama na Afirka ta Kudu, an zabi shi sau da yawa a lambar yabo ta Black Entertainment Television (BET) a Amurka, kuma an taba zaba shi don lambar yabo ta MTV Europe Music Award.

"Abin baƙin ciki ne muka amince da rasuwar ɗanmu , in ji iyayensa Tony da Lynn Forbes a cikin wata sanarwa da aka buga a shafin Twitter na AKA.

Birnin Durban, na Afika ta kudu
Birnin Durban, na Afika ta kudu AFP/Gianluigi Guercia

An harbe shi ne a daren Juma’a tare da wani mutum a lokacin da suke kan hanyarsu ta zuwa motarsu daga wani gidan cin abinci.

“Ana zargin  wasu mutane biyu dauke da makamai ne suka tunkare su daga kan titin inda suka harbe su.

Ba a san dalilin harbin ba, kuma ‘yan sanda na gudanar da bincike.

Ana yawan yin harbe-harbe a Afirka ta Kudu, wadda ke da yawan kisan kai a duniya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.