Isa ga babban shafi

Hukumomin kamaru na tuhumar fitaccen dan kasuwa Jean-Pierre Amougou Belinga

A Kamaru, Fiye da wata daya bayan mutuwar Martinez Zogo, wani dan jarida da aka yi garkuwa da shi, sannan aka kashe shi bayan an azabtar da shi , hukumomin kasar na tuhumar fitaccen dan kasuwa Jean-Pierre Amougou Belinga, da laifin " hadin kai a cikin wannan azabtarwa". 

 Martinez Zogo, dan jarida da ake zargin wasu jami'an gwamnati da kashewa a Kamaru
Martinez Zogo, dan jarida da ake zargin wasu jami'an gwamnati da kashewa a Kamaru © AFP - DANIEL BELOUMOU OLOMO
Talla

An gabatar da Amougou Belinga a cikin daren asabar  a gaban kotun soji da ke Yaoundé babban birnin kasar. Lauyansa Me Charles Tchoungang ya sheidawa manema labarai cewa an garzaya da shi gidan yarin Kondengi inda ake tsare da shi yanzu haka. 

Dan jarida  Martinez Zogo da aka gano gawwar sa a cikin watabn Janairu 2023
Dan jarida Martinez Zogo da aka gano gawwar sa a cikin watabn Janairu 2023 © AFPTV

Leopold Maxime Eko Eko, shugaban hukumar leken asirin waje (DGRE) da daraktan ayyuka Justin Dawe na daga cikin wadanda ake zargin, kamar yadda wani jami'in ma'aikatar sadarwa ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP. 

  Dan kasuwar Belinga zai kasance a karkashin takardar sammaci  a babban gidan yari na Kondengi" bayan "an gabatar da shi a gaban kotu . Wasu muhimman jami’an gwamnati an gabatar da su a gaban kotun soji da yammacin ranar Juma’a, kamar yadda wani dan jarida daga kamfanin dillancin labarai na AFP ya bayyana a nan take. 

Indan aka yi tuni wasu da ba a san ko su wanene ba sun yi garkuwa da Arsène Salomon Mbani Zogo a ranar 17 ga watan Janairu a unguwar da ke wajen babban birnin kasar a gaban ofishin jami'an tsaron Jandarma, Arsène Salomon Mbani Zogo, wanda aka fi sani da "Martinez", mai shekaru 50, an gano gawarsa bayan kwanaki biyar. "A bayyane yake jikinsa ya fuskanci cin zarafi," in ji gwamnati. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.