Isa ga babban shafi

Tshisekedi ya bukaci Faransa ta sanya wa Rwanda takunkumi saboda zargin taimaka wa M23

Shugaban jamhuriyar Dimokradiyyar Congo Felix Tshisekedi ya bukaci Faransa ta gaggauta hukunta Rwanda a ci gaba da tabbatar da zargin da yake yiwa kasar da taimakawa mayakan M23. 

Felix Tshisekedi,shugaban Jamhuriyar DimokaradiyyarCongo.
Felix Tshisekedi,shugaban Jamhuriyar DimokaradiyyarCongo. REUTERS - DENIS BALIBOUSE
Talla

Kalaman na shugaba Tshisekedi na zuwa ne bayan wata ganawa da Emannuel Macron na Faransa a ziyarar da yake yi na wasu kasashen Africa da nufin inganta alakar da ke tsakanin su. 

A cewar sa, daukar mataki kan Rwanda game da ta’azzara rikicin gabashin Goma zai kara yaukaka alakar da ke tsakanin kasar da Faransa. 

Sai dai ko da yake mayar da Martani shugaban na Faransa Macron ya ce akwai bukatar Congo ta kau da kai daga zarge-zarge ta mayar da hankali wajen tunkarar mayakan tare da murkushe su, duk da dai a baya Faransa na cikin kasashen duniya da manyan humomi dake zargin Rwandan da hannu wajen goya wa mayakan baya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.