Isa ga babban shafi

Kakkarfar guguwar Freddy ta kashe mutane 15 a Malawi da Mozambique

Akalla mutane 15 suka mutu a kasashen Malawi da Mozambique sakamakon kakkarfar guguwar da afka musu wadda ta haddasa ruwan sama mai karfi tare da ambaliya lamarin da ya tilasta kwashe tarin mutane don kauce wa karuwar asarar rayuka.

Wani yanki da kakkarrfar guguwar Freddy ta afkawa a Mozambique.
Wani yanki da kakkarrfar guguwar Freddy ta afkawa a Mozambique. LUSA - ANDRÉ CATUEIRA
Talla

Mahukuntan kasashen na Malawi da Mozambique sun sanar da fara aikin kwashe mutanen da ke yankunan da kakkarfar guguwar ta Freddy ta afkawa, bayan kisan mutane 15 tare da bacewar wasu da dama musamman a yankunan da ke gab da teku.

Da sanyin safiyar yau Litinin ne kakkarfar guguwar ta Freddy ta isa Malawi bayan tafka gagarumar barna cikin karshen mako a Mozambique, lamarin da ke nuna dawowar guguwar zuwa kasashen biyu bayan kisan da ta yi a watan jiya.

 

Zuwa yanzu mutane 15 guguwar ta Freddy ta kashe yayinda ake neman wasu da dama da suka bace.
Zuwa yanzu mutane 15 guguwar ta Freddy ta kashe yayinda ake neman wasu da dama da suka bace. LUSA - ANDRÉ CATUEIRA

Guguwar wadda ta haddasa ambaliyar ruwa ta yi awon gaba da tarin gidaje a kasashen biyu, inda rundunar ‘yan sandan Malawi ta sanar da cewar yanzu haka tana laluben mutane fiye da 16 da ruwa ya yi gaba da su a kudancin lardin Blantyre bayan guguwar ta kashe mutane 11 tare da jikkata wasu 4.

Can a Mozambique ma guguwar ta Freddy ta kashe mutane 4 baya ga rushe tarin gidaje da makarantu tun bayan isar ta kasar a asabar din da ta gabata.

Mahukuntan kasashen biyu makwabtan juna sun bayyana yiwuwar karuwar wadanda guguwar ta Freddy ta illata lura da yadda iska mai karfi hade da ruwa ke sake afkawa wasu sassan kasashen a bangare guda kuma ake laluben tarin mutanen da suka bace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.