Isa ga babban shafi

Mahaukaciyar guguwa ta yi sanadin batan kusan mutane dubu 7 a New zealand

Akalla mutane 11 ne suka mutu yayin da dubu 6,400 suka bata a sanadin mahaukaciyar guguwar Cyclone Gabrielle a yankin Kudancin NewZealand.

Mahaukaciyar guguwar Cyclone Gabrielle
Mahaukaciyar guguwar Cyclone Gabrielle @ompsyram via REUTERS - @ompsyram
Talla

Tun ranar 12 ga watan da muke ciki na Fabrairu ne guguwar ta afkawa kasar, lamarin da ya haddasa ambaliyar ruwa mai muni.

Prime ministan kasar Chris Hipkings ya kwatanta guguwar a matsayin babban bala’i mafi muni da kasar ta gani a wannan karni.

A cewar sa akwai yiwuwar samun Karin mutanen da suka mutu, la’akari da yawan mutanen da suka yi batan dabo sanadin guguwar.

Chris Hipkins ya ce guguwar ta shafi rayukan al’umma kai tsaye, yayin da har yanzu ta ki bada damar da za’a fara aikin ceto da lalubo wadanda suka bata, sai yadda guguwar ta lalata hanyoyin sadarwa, turakun wutar lantarki, da gurbata ruwan sha tare da lalata hanyoyi, yayin da ambaliyar ruwa ta shafe wasu yankunan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.