Isa ga babban shafi

BioNTech ya bude karamin sashe a Rwanda don samar da magunguna ga Afrika

Kamfanin harhada magunguna na BioNTech da ke Jamus ya kai wa Rwanda manyan dakunan gwajin magunguna na ''tafi da gidanka'' har guda 6 a wani yunkuri na dakile matsalar karancin kamfanonin sarrafa magungunan da nahiyar Afrika ke fama da su.

Tawagar jami'an kamfanin harhada magunguna na BioNTech da suka kai sundukan sashen harhada magunguna na wucin gadi Rwanda.
Tawagar jami'an kamfanin harhada magunguna na BioNTech da suka kai sundukan sashen harhada magunguna na wucin gadi Rwanda. AP - Andreas Arnold
Talla

Shigar da dakunan gwajin samar da magungunan da kamfanin BioNTech ya yi zuwa Rwanda shi ne irinsa na farko da aka taba gani a tarihi, dakunan da aka samar da su daga sundukan dakon kayan da aka sake sarrafawa wadanda ake saran za a jere su don samar da katafaren kamfanin samar da magunguna ko kuma alluran rigakafin cutuka daban-daban a birnin Kigali fadar gwamnatin kasar.

Shugaban sashen tsare-tsare na BioNTech Sierk Poetting ya ce nasarar shigar da dakunan gwajin na ''tafi da gidan ka'' babban ci gaba ne a kokarin habaka samar da magunguna don dakile barazanar cutuka a nan gaba.

Tun bayan bullar annobar cutar Covid-19 da ta kassara tsarin lafiya da kamfanonin samar da magungunan kasashe, ya fito karara yadda nahiyar Afrika ke da karancin kamfanonin samar da magungunan cutuka, wanda ya sanya ta dogara da kasashen ketare don samun magunguna da rigakafin cutuka.

Hukumar yaki da cutuka masu yaduwa ta Afrika CDC ta ce har zuwa yanzu kasa da kashi 50 na yawan al’ummar Afrika biliyan 1 da miliyan 200 ne kadai suka samu cikakkiyar kariya daga cutar Covid-19.

A cewar BioNTech dakunan harhada magungunan na Kigali na da zarafin iya samar da alluran rigakafi fiye da miliyan 100 cikin watanni 12 na farkon fara aikinsa ko da ya ke zai dauki tsawon shekara guda gabanin aikinsa ya kankama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.