Isa ga babban shafi

Guguwar Freddy ta hallaka sama da mutane 100 a Mozambique da Malawi

Al’ummomin Mozambique da Malawi na cikin jimamin hasarar rayuka da na dimbin dukiyar da suka tafka a dalilin guguwar Freddy, wadda ta halaka mutane fiye da 100, gami da jikkata wasu daruruwa, baya ga dukiya mai tarin yawa da ta lalata, a lokacin da ta sake afka wa kasashen biyu da ke kudancin Afirka.

Wasu daga cikin wadanda guguwar Freddy ta shafa.
Wasu daga cikin wadanda guguwar Freddy ta shafa. REUTERS - ELDSON CHAGARA
Talla

A baya bayan nan kwararrun hukumar hasashen yanayi ta duniya, suka yi gargadin cewa guguwar ta Freddy, za ta iya kafa tarihin zama mafi dadewa da aka gani tana kadawa babu kakkautawa, bayan da ta shafe fiye da kwanaki 22 tana ratsa yankuna da karfinta dauke da ruwan sama kamar da bakin kwarya.

A ranar Asabar da ta gabata, da karfin tsiya guguwar ta rinka yaye rufin gine-gine a yankin tsakiyar Mozambique, ya yin da ta haddasa ambaliyar ruwa a babbar tashar jiragen ruwa ta Quelimane, inda daga nan ta dangana da kasar Malawi dauke da ruwan sama mai karfin da ya haddasa zaftarewar kasa.

Kawo yanzu dai babu cikakkun alkaluma kan adadin rayuka da kuma hasarar dukiyar da guguwar Freddy ta haddasa a Mozambique, sakamakon katsewar layukan waya da wutar lantarki a wasu daga cikin yankunan da iftila’in ya shafa.

Sai dai a Malawi, jami’an agaji sun ce mutane 99 guguwar ta halaka, cikinsu har da  85 da suka mutu a birnin Blantyre da ke zama  cibiyar kasuwancin kasar.

A jumlace dai mutane 136 guguwar Freddy ta halaka a Mozambique, Malawi da kuma Madagascar, tun bayan da ta fara afka wa kasashen uku a watan Fabarairun da  ya  gabata. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.