Isa ga babban shafi

Sakataren harkokin wajen Amurka na ziyarar ba zata a Jamhuriyar Nijar

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fara ziyarar aiki a Jamhuriyar Nijar domin tattauna batutuwan da zasu bunkasa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. 

Sakataren harkokin wajen Amurka kenan, Antony Blinken.
Sakataren harkokin wajen Amurka kenan, Antony Blinken. © AFP - PETR DAVID JOSEK
Talla

Antony Blinken ne babban jami’in gwamnatin Amurka na farko da ya ziyarci Nijar wadda kasar Faransa ta yiwa mulkin mallaka, wadda kuma ke dauke da sojojin manyan kasashen guda 2 dake yaki da ‘yan ta’adda a yankin Sahel. 

Ana saran Sakataren ya bayyana taimakon Amurka ga Nijar, yayin da ake bayyana cewar ziyarar zata zama wata damar nuna goyan baya akan irin matakan da gwamnatin Jamhuriyar Nijar a karkashin shugaba bazoum Mohammed ke dauka, musamman ganin yadda yake sukar kamfanin sojojin hayar Wagner mallakar kasar Rasha, wadanda ke ci gaba da kutse a wasu kasashen Afirka. 

Wata babbar jami’ar gwamnatin Amurka dake rakiyar Blinken ta shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewar gwamnatin Nijar na kan turba mai kyau, saboda haka zasu taimaka muta wajen magance barazanar da take fuskanta a yankin. 

Kasar Amurka na bukatar ganin ta taimakawa Jamhuriyar Nijar inganta bangaren sojin ta, musamman wajen ganin na rage yadda ake asarar rayukan fararen hula lokacin yaki da ta’addanci. 

Jami’ar tace babu tantama Nijar na cikin tsaka mai wuya, amma duk da haka shugabannin kasar na daukar matakan da suka dace wajen shawo kan matsalolin da suke fuskanta. 

Ta kuma bayyana kasar a matsayin wadda matsalar sauyin yanayi ya yiwa illa wajen ganin tana rasa akalla eka 250,000 na filayen nomanta kowacce shekara. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.