Isa ga babban shafi
Nijar-Amurka

'Yan bindigar da suka yi garkuwa da Ba'amurke a Nijar sun nemi diyya

'Yan Bindigar da suka sace wani dan kasar Amurka Philip Walton a Jamhuriyar Nijar shekaran jiya Talata, sun bukaci a ba su diyya domin sakin sa.

An dai bayyana Ba'amurke da 'da a wajen wani mai Bushara da ke zaune a kasar ta Nijar.
An dai bayyana Ba'amurke da 'da a wajen wani mai Bushara da ke zaune a kasar ta Nijar. Jakarta Globe
Talla

Wasu Yan bindiga guda 6 dauke da bindigogi kirar Kalashnikov ne suka sace Walton a wajen kauyen Massalata, kuma an bayyana shi a matsayin ‘da ne ga wani mai bushara da ke zama a kasar.

Ofishin Jakadancin Amurka da ke Yamma ya sanar da sace Walton wanda dan kasar ne, kuma ya ce suna taimakawa iyalan sa kamar yadda doka ta tanada.

Ma’aikatar harkokin cikin gidan Nijar ta ce Yan bindigar da suka sace Walton, sun gudanar da bincike akan sa kafin tserewa kusa da iyakar kasar.

Sanarwar gwamnatin ta ce an kara yawan jami’an tsaro a yankin, yayin da ake hada kai da ofishin Jakadancin Amurka da kuma hukumomin tsaron Najeriya domin ganin an kubutar da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.