Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta kasance kan gaba wajen tabarbarewar ilimi a Afirka - UNICEF

Kusan kaso daya cikin hudu na makarantu aka rufe a Burkina Faso saboda rashin tsaro da tashe-tashen hankula, a cewar wata kungiya mai zaman kanta ta kasar Norway, daidai lokacin da ake samun karuwar hare-haren masu tayar da kayar baya a kasar.

Balkissa Barro 'yar sheakru 10 daga tsakiya, tare da wasu yara a kan hanyarsu ta zuwa makaranta a kauyen Dori da ke Burkina Faso.
Balkissa Barro 'yar sheakru 10 daga tsakiya, tare da wasu yara a kan hanyarsu ta zuwa makaranta a kauyen Dori da ke Burkina Faso. AP - Sam Mednick
Talla

A watan da ya gabata makarantu 6,134, aka rufe, inda aka samu karuwar kashi 44 cikin 100 tun daga watan Mayu, in ji Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Norway.

Sama da yara miliyan daya ne yanzu haka basa zuwa makaranta a Burkina Faso, in ji sanarwar, inda ta kara da cewa wadannan matasa sun kasance cikin rudani saboda gudun hijira da rikice-rikice.

Wakiliyar hukumar kula da kananan yara ta Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF Sandra Lattouf, ta yi gargadin cewa yaran da ba sa zuwa makaranta na cikin barazanar fatauci ko kuma yaudarar su shiga kungiyoyin da ke dauke da makamai.

Kungiyar ta ce Burkina Faso ta kasance kan gaba daga cikin kasashen da aka rufe makarantu a tsakiya da yammacin Afirka.

Rufe makarantu a kasar dai ya shafi malamai sama da 31,000, ko da yake yanzu haka an rarraba wasu malamai 6,300 daga cikinsu aka tura ssu aiki wasu wuraren.

Burkina Faso da ta kasance daya daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya, na fama da tashe tashen hankula da suka barke daga makwabciyarta Mali a shekarar 2015.

Kusan kashi 40 na kasar Burkina Faso na karkashin ikon masu tayar da kayar baya, abin da ya fusata sojojin kasar gudanar da juyin mulki har sau biyu a bara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.