Isa ga babban shafi

Ganduje ya nemi gafara a wurin Kanawa

Gwamnan Jihar Kano dake Najeriya, Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci jama’ar jihar da su masa aikin gafara, musamman wadanda ya batawa lokacin mulkinsa.

Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje. Premium Times
Talla

Ganduje wanda ya bukaci gafarar lokacin da ya halarci wajen tafsiri a Masallachin Al-furqan dake birnin Kano, yace ganin wa’adin mulkinsa yazo karshe, yana bukatar jama’ar jihar su yafe masa, kuma shima ya yafewa duk wanda ya saba masa. 

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Solacebase

Gwamnan yayi amfani da wannan dama wajen ban kwana da jama’ar jihar da kuma musu fatan alkhairi ganin cewar a ranar 29 ga watan gobe zai mika mulki ga Abba Kabir na Jam’iyyar NNPP wanda ya samu nasara a zaben da akayi a watan jiya. 

Ganduje ya kwashe shekaru 8 a karagar mulki a matsayin zababben gwamnan jihar Kano, bayan shekaru 8 da yayi yana yiwa Dr Rabiu Musa Kwankwaso mataimakin gwamna. 

Gwamnan Jihar Kano  Abdullahi Umar Danduje
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Danduje © rfi hausa

Masana siyasa na kallonsa a matsayin daya daga cikin wadanda suka kwashe dogon lokaci a sha’anin mulkin jiha, kuma daya daga cikin wadanda gwamnonin da suka yi aiki da su suka baiwa kujerar gwamna sabanin yadda ake gani a siyasar Najeriya. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.