Najeriya: Ana gudanar da zabukan cike gurbi a jihohi 24 na kasar
A Najeriya, yau Asabaar ake gudanar da zabukan cike gurbi a mazabu 2660 a kananan hukumomi 185 a cikin jihohi 24 na kasar.
Wallafawa ranar:
Ana gudanar da zabukan gwamna da na ‘yan majalisun dokoki a jihohin Adamawa da Kebbi, saboda haka ne ma babban sufeto janar na ‘yan sandan kasar Usman Baba, ya yi umurnin a jibge dimbim jami’an ‘yan sanda da kayan aiki don tabbatar da an gudanar da zabukan lafiya.
Hankula za su fi karkata a jihohin Adamawa, Kebbi na arewacin kasar, inda za a sake zabukan gwamnoni bayan da aka ta ayyana su a matsayin wadanda ba su kammalu ba a zaben 11 ga watan Maris.
Za a gudanar zaben cike bgurbbi na gwamna a mazabu 142 a fadin kananan hukumomi 20 na jihar Kebbi, kuma zai kasance aranagama tsakanin jam’iyyar APC da na PDP ne.
Aayyana zaben da aka yi tun da farko a jihar a matsayin wanda bai kammalu ba, biyo bayan soke sakamakon zabe kananan hukumomi 20 daga cikin 21 na jihar.
Kafin ayyana zaben a matsayin wanda bai kammalu ba, dan takarar jam’iyyar APC, Dokta Nasir Idris nne ke kan gaba da kuri’u, 388,258 a yayin da Janar Aminu Bande na jam’iyyar PDP ke biye da kuri’u 342,980.
A jihar Adamawa, za a gudanar da zaben cike gurbi a kanana hukumomi 20 don tabbatar da wanda zai dare kujerar gwamnan jihar a tsakanin gwamna mai ci, Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP da Sanata Aishatu Binani ta jam’iyyar APC.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu