Isa ga babban shafi

Afirka za ta iya dogaro da mu wajen yakar ayyukan ta'addanci - Faransa

Faransa kuma kungiyar Tarayyar Turai EU sun jaddada kudurinsu na yakar ayyukan masu tayar da kayar baya a nahiyar Afirka, daiddai lokacin da wasu kasashe renon Faransa suka fara nuna shakku kan kasar, yayin da wasu daga cikinsu kuma suka yi mata tawaye, da sunan nemanrwa kan su mafita.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron
Shugaban Faransa Emmanuel Macron via REUTERS - POOL
Talla

Sakatariyar Harkokin Ci Gaban Faransa, Chrysoula Zacharopoulou , wadda ta kai ziyara Cibiyar Yaki da Ta'addanci ta kasa da kasa da ke Jacqueville, a Abidjan, wato inda ake horar da sojojin Afirka domin yakar masu tayar da kayar baya,  ta ce Faransa ba ta goyon bayan cin zarafin da ke faruwa a nahiyar.

Faransa dai ta ce kasashen nahiyar za su iya dogaro da ita daidai lokacin da wasu kasashe ke ci gaba da kaddamar da shirin hadin gwiwar tsaro ta hanyar amfani dakarun sa-kai, da kuma dakarun kamfanin Wagner, na kasar Rasha.

Zacharopoulou ta kasance wakiliyar Faransa a cikin kwamitin gudanarwa na farko na AILCT wanda Faransa da Cote d'Ivoire suka kirkira a shekarar 2021, daga bisani kungiyar EU, Tarayyar Afirka, Kungiyar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), Canada, Netherlands, Spain, Australia, Switzerland, da kuma Amurka suka shiga suma, domin yakar ayyukan ta’addanci.

A yammacin Afirka, Cote d'Ivoire na daya daga cikin kawayen Faransa na karshe a yakin da ake yi da masu dauke da makamai tun bayan ficewar sojojin Faransa daga Mali da Burkina Faso, wadanda shugabanninsu, wato Assimi Goïta da Ibrahim Traoré, suka bukaci hakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.