Isa ga babban shafi

Tawagar Commonwealth ta isa Saliyo don sanya ido kan zaben kasar

Tawagar Kungiyar Kasashe Renon Ingila ta Commonwealth ta isa Saliyo domin sanya ido kan yadda zaben shugaban kasar da za a yi makon gobe zai gudana. 

Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, shi ya jagoranci tawagar.
Tsohon Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo, shi ya jagoranci tawagar. © Yemi Osinbajo
Talla

Tawagar wadda ke karkashin jagorancin tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo, za ta gana da shugaban hukumar zabe da shugabannin jam’iyyun siyasar kasar da kuma kungiyoyin fararen hula kan shirin zaben. 

Yanzu haka 'yan takara biyu ne ke sahun gaba a fafatawar da ake yi a zaben da zai gudana ranar 24 ga watan nan, wadanda suka hada da shugaba mai ci Julius Mado Bio da ke neman zarcewa, tare da tsohon abokin karawarsa Samura Kamara, wanda ya zo na biyu a zaben shekarar 2018 wanda Bio ya samu nasara. 

Ana sa ran gudanar da zaben ‘yan majalisun dokoki da na kananan hukumomi yayin gudanar da zaben shugaban kasar ranar 24 ga wata. 

Masu kada kuri’u miliyan 3 da dubu 374 da dari 258 ake sa ran su zabi shugaban kasar da ‘yan majalisu, wanda ya nuna samun sabbin masu zabe dubu 195 da 595 akan rajistar shekarar 2018. 

Sai dai tuni shugaban ‘yan adawar kasar, Samura Kamara ya zargi shugaban hukumar zabe da yunkurin tafka magudi, inda ya bukace shi da ya sauka daga jagorancin hukumar. 

Kamara ya yi zargin cewar hukumar zaben ba ta da shirin gudanar da sahihin zabe, saboda haka suna bukatar shugaban ta Mohammed Kone da ya aje mukaminsa tare da na kwamishohin hukumar, domin maye gurbinsu da wasu sabbi. 

Yanzu dai haka shugaban ‘yan adawar Kamara na fuskantar zargin cin hanci da rashawar da ka iya hana shi tsayawa takara muddin aka tabbatar da laifi akansa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.