Isa ga babban shafi

Masu sanya ido ba su gamsu da sakamakon zaben Saliyo ba

Tawagar ‘yan kallo na cikin gida da kuma na kungiyar Tarayyar Afrika da suka sanya ido a zaben shugabancin kasar Saliyo, sun ce akwai bambanci mai rata tsakanin alkaluman da hukumar zabe ta sanar da ke bayyana Julius Maad Bio a matsayin wanda ya lashe zaben shugabancin kasar da kuma alkaluman da aka tattara a karshen zaben makon jiya. 

Masu sanya ido ba su gamsu da sakamakon zaben Saliyo ba.
Masu sanya ido ba su gamsu da sakamakon zaben Saliyo ba. © COOPER INVEEN / REUTERS
Talla

Yayin da tuni aka rantsar da Maada Bio domin shugabancin kasar wa’adi na biyu, Ausgustine Sorie Marrah, lauya kuma masanin dokoki a Saliyo ya ce halin da kasar ta shiga a yau, na nuni da cewa akwai bukatar yi wa kundin tsarin mulkin kasar gyara.   

Wannan yana nufin cewa duk wanda ya fadi a zabe ko yake da shakka a game da galabar akobin hamayyarsa, yana da damar zuwa kotun koli kafin rantsar da wanda ya yi nasara, daga nan kuma kotu ce za ta dauki matakan da suka dace. Inji Marraah.  

Masanin dokokin ya kara da cewa "A kodayaushe kotun koli tana da hurumin binciken sakamakon zaben, sannan kuma tana iya soke shi. Na san cewa akwai mutanen da ke tunanin cewa hakan ba zai taba yiyuwa ba, saboda wai a tunaninsu dan takarar da aka bayyana cewa ya lashe zaben zai iya amfani da matsayinsa domin karkata ra’ayoyin alkalamn kotun kolin."

Kimanin shekaru 10 kenan da masu raji ke fafutukar ganin an samar da sauyi a kundin tsarin mulkin kasar dangane da batun zaben kasar.  

Mutane da dama na da ra’ayin cewa kundin tsarin mulki na shekarar 1991 da Sierra Leone ke amfani da shi, bai dace da kasar ba a yau. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.