Isa ga babban shafi

An sallami shugaban hukumar kula da ingancin magunguna ta Gambia

Gwamnatin Gambia ta sanar a jiya Juma’a cewa maganin tari guda hudu da aka shigo da su daga Indiya ne suka yi sanadiyar mutuwar akalla yara 70 sakamakon ciwon koda a bara.

Wasu daga cikin yara da aka girke a sansanin yan gudun hijira  a Gambia
Wasu daga cikin yara da aka girke a sansanin yan gudun hijira a Gambia AFP - MUHAMADOU BITTAYE
Talla

Ministan lafiya na kasar Dr Ahmadou Lamin Samateh ya shaidawa taron manema labarai cewa, an samu gazawa wajen tabbatar da ingancin magunguna da aka shigo da su, inda ya soki tsarin da kuma kalubalantar aikin da ya shafi bangaren rajistar kayayyakin daga hukumar kula da lafiya ta kasar  wato (MCA).

An sallami shugaban hukumar ta MCA, yayin da Ministan  ya kuma zargi mai kula da harhada magunguna wanda ya ba da izinin shigo da magungunan ba tare da bayar da isassun bayanan a kai.

Tun a watan Satumban bara, Gambia ta ba da umarnin a dawo da magungunan tari da sanyi da dama, da kuma duk wani kayayyakin da cibiyar binciken magunguna ta Indiya ta kera daga inda gurbatattun syrup din ya samo asali, bayan mutuwar jarirai akalla 70.

Daga baya ta dakatar da duk samfuran kamfanin Indiya.

Wasu daga cikin magunguna na jabu da aka shigo da su Gambia
Wasu daga cikin magunguna na jabu da aka shigo da su Gambia AFP - MILAN BERCKMANS

A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO), gwaje-gwajen da aka yi  sun gano "adadin da ba za a yarda da su ba" na diethylene glycol da ethylene glycol, wadanda aka saba amfani da su azaman maganin daskarewa kuma suna iya yin kisa idan an sha.

Tawagar ta Gambia ta yi nuni da cewa akwai bukatar a gaggauta kafa dakin gwaje-gwaje masu inganci don gudanar da gwaje-gwaje kan duk magungunan da ake shigowa da su cikin kasar, wanda hukumar ta WHO ke bayar da tallafi don kafawa.

Samateh ya ce ya kuma ba da shawarar inganta tsarin kiwon lafiyar kasar da ya hada da kafa makarantar hada magunguna da tsaurara dokoki kan magunguna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.