Isa ga babban shafi

An kama karin sojojin da ake zargi da yunkurin juyin mulki a Gambia

Gambia ta kafa kwamitin bincike, wanda ta baiwa kwanaki 30 domin ya ba da rahoto kan yunkurin juyin mulkin da aka yi a makon da ya gabata, inda ta kama karin sojoji.

Shugaban kasar Gambia Adama Barrow.
Shugaban kasar Gambia Adama Barrow. AFP - MUHAMADOU BITTAYE
Talla

A ranar Talata aka rantsar da kwamitin binciken mai mutane 11 da suka hada da jami’an ma'aikatar shari'a, da ofishin tsaron kasa, da sojoji, da 'yan sanda da na leken asiri.

A ranar Larabar da ta gabata gwamnatin kasar ta Gambia ta ce ta dakile yunkurin juyin mulki, tare da tsare wasu jami’an soji.

Kakakin gwamnati Ebrima Sankareh ya ce, an tsare wani Kaftin da Laftanar a karshen mako kuma suna taimakawa masu bincike don gano masu sauran masu hannu a yunkurin na hambarar da gwamnatin Shugaba Adama Barrow.

Kawo yanzu sojoji biyar aka tsare da kuma wasu mutane biyu da ake zargi da taka rawa a yunkurin juyin mulkin.

Shi ma dai madugun ‘yan adawa Momodou Sabally wanda ya kasance tsohon ministan tafiyar da harkokin fadar shugaban kasa a karkashin tsohon shugaba Yahya Jammeh ya shiga hannu, bayan da ya fito a wani faifan bidiyo yana nuni da cewa za a hambarar da shugaba Barrow kafin zaben kananan hukumomi da ke tafe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.