Marocco ta ceto bakin haure sama da 50 dake kokarin shiga Spain
Sojojin ruwan kasar Morocco sun kama bakin haure sama da 50 daga yankin kudu da hamadar sahara a gabar tekun kudancin kasar, a daidai lokacin da ake samun karuwar kwararar ‘yan ciranin zuwa kasar Spain.
Wallafawa ranar:
Kamfanin dillancin labaran MAP ya ruwaito majiyar sojan kasar, ta na cewa, "Rundunar sojojin ruwa ta Royal da ke sintiri a kusa da Tan-Tan a ranar Talata sun taimaka wa bakin haure 56 da ba su samu damar tsallakawa ba daga yankin kudu da hamadar Saharar Afirka a cikin wani karamin kwale-kwale."
Sanarwar rundunar sojin Morocco tace, bakin hauren "sun sami agajin farko a cikin jirgin, kafin a kwashe su cikin koshin lafiya zuwa tashar jiragen ruwa na Tan-Tan, sannan a mika su ga jami'an tsaron Jandarma domin gudanar da ayyukan da suka saba".
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai rundunar tsaron gabar ruwan Morocco ta sanar da gano gawarwakin wasu 'yan ci-rani biyar 'yan kasar Senegal tare da ceto wasu 189 da kwale-kwalen su ya kife a ranar Asabar a kusa da Guerguerat da ke yammacin Sahara a kudancin kasar Morocco.
Akalla bakin haure 'yan kasar Senegal 13 ne suka mutu a tsakiyar watan Yuli lokacin da jirginsu ya nutse a gabar tekun Morocco, a cewar hukumomin kasar Senegal.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu