Isa ga babban shafi

Morocco ta fara gurfanar da bakin-hauren da suka yi kokarin shiga Spain

Mahukuntan kasar Morocco sun fara gurfanar da bakin-haure 65 a gaban kotun, wadanda suka yi yunkurin tsallakawa kasar Spain a ranar Juma'a, ta hanyar kutsawa kan iyakar kasar, lamarin da ya yi sanadin mutuwar bakin-hauren akalla 23, kamar yadda wata majiyar shari'a ta bayyana a ranar Litinin.

Mutane yayin zanga-zanga a birnin Madrid kan mutuwar bakin-haure akalla 23 a ranar Juma'a yayin yunkurin na isa yankin Melilla na kasar Spain a ranar 26 ga Yuni, 2022.
Mutane yayin zanga-zanga a birnin Madrid kan mutuwar bakin-haure akalla 23 a ranar Juma'a yayin yunkurin na isa yankin Melilla na kasar Spain a ranar 26 ga Yuni, 2022. © REUTERS/Nacho Doce
Talla

Kimanin bakin-haure 2,000 ne suka yunkurin tsallakawa cikin Spain da karfin tsiya daga arewacin Morocco, lamarin da ya haifar da kazamin fada tsakaninsu da jami'an tsaron Morocco da masu tsaron kan iyaka na Spain a yankin Melilla, inda ‘yan ci ranin kusan 100 suka yi nasarar tsallakewa.

Mahukuntan kasar Morocco sun ce mutuwar bakin-hauren da dama ta biyo bayan tirmitsitsin da aka yi yayin arrangamar ta su, yayin da kuma wasu daga cikinsu suka mutu, sakamakon fadowar da suka yi, daga kan katanga mai tsayi.

Alkaluman da jami’an tsaron suka bayar a karshen mako, sun nuna cewar abokan aikinsu akalla 140 ne suka jikkata, tare da bakin-haure 76 a ranar Juma’ar da ta gabata wato 24 ga watan Yuni.

Kungiyar kare hakkin Dan Adam ta kasar Morocco AMDH ta ce bakin haure 29 ne suka mutu, a cewar wasu majiyoyin asibiti da ba a bayyana sunayensu ba.

A ranar Lahadin da ta gabata, kungiyar Tarayyar Afirka AU ta bayyana kaduwarta kan abin da ta kira musgunawa bakin-haure da ya haddasa rasa rayuka da kuma jikkatar wasu da dama, inda ta bukaci a gudanar da bincike cikin gaggawa kan lamarin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.