Isa ga babban shafi

'Yan sanda fiye da 140 sun jikkata yayin kokarin hana bakin-haure shiga Spain

Jami’an tsaron kan iyaka na Spain sun ce, bakin-haure biyar sun rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata, a lokacin da dimbin bakin hauren suka yi kokarin tsallakawa daga Morocco zuwa cikin yankin Melilla na kasar Spain a ranar Juma'a.

Wasu daga cikin bakin-hauren da suka tsallaka iyaka zuwa cikin Spain daga Morocco.
Wasu daga cikin bakin-hauren da suka tsallaka iyaka zuwa cikin Spain daga Morocco. AP - Javier Bernardo
Talla

Gwamnatin Spain ta ce, akalla bakin haure 2,000 ne suka tunkari Melilla da asuba, kuma sama da 500 sun sami nasarar shiga yankin daga cikin Morocco, bayan da suka yanke shingen wayar da ya raba kan iyakar da suka tsallaka.

Kididdiga ta nuna cewar mutane 130 daga cikin bakin-hauren ‘yan Afirka ne daga yankin Kudu da saharar Afirka dukkaninsu maza.

Wani jami'in kasar Morocco daga garin Nador da ke kusa da kan iyaka ya ce jami'an tsaro 140 da bakin-haure 76 ne suka jikkata yayin arrangamar da suka yi, a lokacin da suke yunkurin tsallaka kan iyakar, zuwa cikin Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.