Isa ga babban shafi

Sojojin Gabon sun sanar da juyin mulki bayan soke sakamakon zabe

Dandazon sojojin Gabon da suka bayyana a gidan talabijin din kasar na Gabon 24 sun sanar da kwace iko daga gwamnati mai ci tare da rushe sakamakon zaben da aka bayyana Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya lashe.

Sojojin da suka jagoranci juyin mulki a Gabon.
Sojojin da suka jagoranci juyin mulki a Gabon. © AFP
Talla

Kafin sanarwar sojojin, bayanai sun ce an shafe tsawon sa’o’i ana jiyo karar harbin bindiga a sassan Libreville babban birnin kasar ko da ya ke babu tabbacin ko musayar wuta ce ko kuma kawai sojojin na harbin iska ne.    

Guda cikin Sojojin su akalla 12 da ya gabatar da jawabin kai tsaye ta gidan talabijin din da safiyar yau Laraba, ya sanar da rushe dukkanin sassan gwamnati ciki har da majalisun dokoki da kuma kotun kundin tsarin mulki.

A cewar Sojan wanda ba a kai ga bayyana sunansa ba, ba su gamsu da yadda zaben shugaban kasar ya gudana ba, kuma za su kawo karshen tarnakin da kasar ke fuskanta.

Dambarwa ta kaure a Gabon ne tun bayan kammala zaben shugaban kasar, wanda ya kai ga katse Intanet da kuma sanya dokar hana fita, lamarin da bangaren adawa ya kira da yunkurin tafka magudi.

Lamarin ya tsananta ne bayan hukumar zaben kasar ta sanar da shugaba Ali Bongo Ondimba a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar duk da yadda bangaren adawa ke ikirarin samun rinjayen kuri’u.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.