Isa ga babban shafi

Abubuwan da sabon shugaban mulkin sojin Gabon zai yi wa kasar

Sabon shugaban mulkin sojin Gabon da ya sha rantsuwar kama aiki a wannan Litinin Janar Brice Nguema ya yi alkawarin gudanar da sahihin zabe domin maido da mulkin farar hula duk da cewa, bai tsayar da ranar shirya zaben ba.

Sabon shugaban mulkin sojin Gabon Brice Oligui Nguema jim kadan da shan rantsuwar kama-aiki a wannan Litinin.
Sabon shugaban mulkin sojin Gabon Brice Oligui Nguema jim kadan da shan rantsuwar kama-aiki a wannan Litinin. © AFP
Talla

Kazalika sabon shugaban ya yi alkawarin yin afuwa ga fursunonin siyasa, yana mai jaddada cewa, juyin mulkin da suka yi, ya ceci Gabon daga zubar da jini bayan gudanar da zaben da ya ce, na cike da murdiya da kurakurai.

A ranar Laraba da ta gabata ne, Oligui wanda shi ne shugaban dakarun tsaron fadar shugaban kasa, ya jagoranci hambarar da gwamnatin Ali Bongo Ondimba wanda iyalansa suka shafe tsawon shekaru 55 suna shugabancin kasar mai arzikin man fetur.

Juyin mulkin na zuwa ne bayan hukumar zabe ta ayyana  Bongo mai shekaru 64 a matsayin wanda ya sake yin nasarar a zaben na shugaban kasa, zaben da 'yan adawa suka yi watsi da sakamakonsa.

 

Janar Oligui jim na karbar rantsuwar kama aiki a wannan Litinin.
Janar Oligui jim na karbar rantsuwar kama aiki a wannan Litinin. REUTERS - STRINGER

 

Sabon shugaban na mulkin soji ya nemi hadin-kan daukacin manyan kungiyoyin Gabon domin rubuta sabon kundin tsarin mulkin kasar wanda ya ce, za a rubuta bayan gudanar da kuri'ar jin ra'ayin jama'a.

Oligui mai shekaru 48, sanye da jan kakin soji na musamman, ya ce, zai umarci gwamnatin kasar da za ta zo nan gaba da ta muhimmanta yin afuwa ga fursunonin siyasa tare da saukaka wa mutanen da suka gudu dawowa cikin kasar.

Matsin lambar da sabon shugaban ke fuskanta

Kasashen duniya da dama ba su amince da Oligui a matsayin halastaccen shugaban Gabon ba, yayin da yake fuskantar matsin lamba don ganin ya janye shirinsa na maido da mulki ga farar hula.

Sai dai Oligui ya kare matsayinsu na yin juyin mulkin, yana mai cewa, sojojinsa sun aikata haka ne domin kare rayukan al'umma.

Mun yi matukar mamaki kan yadda muka ji cewa, wasu kungiyoyin kasashen duniya sun yi Allah-wadai da matakin da sojoji suka dauka, wadanda ke mutunta alkawarin da suka yi na kare rayukan 'yan kasar.

Sabon shugaban mulkin sojin ya caccaki kasashen duniya da wasu manyan kungiyoyin duniya da ke sukar juyin mulkin da suka yi a Gabon.

Gabon ta bi sahun Mali da Guinea da Sudan da Burkina Faso da Nijar da aka ayyana su a matsayin kasashen duniya da suka yi fama da juye-juyen mulki a cikin shekaru uku da suka gabata, al'amarin da ke tayar da hankulan shugabannin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.