Girgizar kasa: Za a yi makokin kwanaki 3 a Morocco bayan mutuwar mutane sama da 2000
Sarkin Morocco, Mohamed Na Shida ya ayyana kwanaki 3 na makoki a fadin kasar don juyayin wadanda kakkarfar girgizar kasa da aka yi a kasar ranar Juma’a ta rutsa da su.
Wallafawa ranar:
Wata sanarwa daga masarautar Morocco ta ce za a saukar da tutar kasar kasa-kasa a dukkannin gine-ginen gwamnati a ilahirin kwanakin da za a shafe ana makokin.
Sarkin na Morocco ya kuma yi umurnin kafa wani kwamiti na ministoci da zai tsara shirin sake gina gidajen da suka lalace sakamakon wannan girgizar kasa mai karfin maki 6 da digo 8.
Sama da mutane dubu 2 ne suka mutu, a yayin da fiye da dubu 1 suka jikkata sakamakon wannan girgizar kasa da ta auku ranar Juma’a.
Wadanda suka mutu sakamakon wannan girgiszar kasa suna yankuna dabam-dabam ne da suka hada da Al Haouz da Marrakesh, da kuma biranen Ouarzazate, Azilal, Chichaoua, da Taroudant, kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar cikin gidan kasar ta bayyana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu