Isa ga babban shafi

Mun gamsu da wa'adin sojoji na shirya zabe a Gabon - Ndong

Sabon Prime ministan Gabon Raymond Ndong Sima ya goyi bayan sanarwar sojoji na bukatar shekaru biyu kafin shirya zaben da zai mayar da iko hannun farar hula a kasar, yana mai cewa shekaru biyu adadin lokaci ne da hankali zai iya dauka.

Sabon Prime ministan Gabon Raymond Ndong Sima
Sabon Prime ministan Gabon Raymond Ndong Sima AFP - -
Talla

Yayin tattaunawar sa da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, Prime minista Sima ya ce wannan kankanin adadi da sojoji suka bukata, ya nuna yadda suka sanya ci gaba kasa a gaban su fiye da bukatar dawwama akan mulki.

A cewar sa akwai kyakyawan fatan cewa sojojin zasu fitar da kyakyawan tsarin yadda za’a gudanar da zabe mai inganci cikin shekaru biyun da suka bukata.

To amma wasu kalamai da suka dauki hankali yayin tattaunawar shine yadda yace watakila za’a iya samun kari ko kuma ragi a cikin watanni 24 da sojojin suka bukata, abinda ke nuna akwai lam’a a cikin jawaban sa.

Tun bayan juyin mulkin ne kasashen duniya ke yabawa sojojin la’akari da yadda suke bayar da hadin kai wajen tattaunawa da kuma duba yadda za’a mayar da mulki hannun farar hula ba tare da wata matsala ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.