Isa ga babban shafi

Morocco ta yi watsi da agajin kungiyar Red Cross ta Jamus

Kungiyar agaji ta Red Cross a Jamus ta ce dole ta tilasta mata karkatar da kayakin agajin da ta nufaci kai wa Morocco saboda sharuddan da kasar ta gindaya gabanin karbar kayakin agaji daga kungiyar ta DRK.

Har zuwa yanzu jami'an agaji basu iya kaiwa ga yankunan kan tsaunukan kasar ta Morocco ba, saboda rashin kyawun hanyoyi.
Har zuwa yanzu jami'an agaji basu iya kaiwa ga yankunan kan tsaunukan kasar ta Morocco ba, saboda rashin kyawun hanyoyi. REUTERS - HANNAH MCKAY
Talla

Sanarwar da kungiyar agajin ta Jamus ta fitar yau alhamis ta ce dole ta tilasta jirginta makare da kayakin agaji ci gaba da zama a filin jirgin zaman birnin Lipzig wanda aka tsara ya tashi yau alhamis bayan da mahukuntan Morocco suka gindaya sharuddan da suka wuce karfin ikon kungiyar agajin ta Red Cross.

A cewar kungiyar abin takaici ne yadda suka gaza isar da kayakin aagajin na su duk da yadda dubunnan mutane ke halin tsananin bukatar agaji a Morocco.

Kakkarfar girgizar kasa mai karfin maki 6.8 ta afkawa Morocco a daren juma’ar da ta gabata wayewar asabar, wadda ta kashe mutane akalla dubu 3, kuma har zuwa yanzu wasu ke ci gaba da kasancewa a karkashin baraguzan gine-gine, musamman a kauyukan da ke yankunan tsaunukan Atlas.

Sai dai Morocco ta ki amincewa da karbar agaji daga da dama daga cikin kasashen da suka nemi su kai dauki ga jama’arta, ciki kuwa har da Faransa da Jamus.

A talatar da ta gabata ne, kungiyar at Red Cross a Jamus ta kafa wata gidauniyar tattara dala miliyan 100 don taimakawa wadanda gigizar kasar ta tagayyara a Morocco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.