Isa ga babban shafi

An cire rai daga yiwuwar ceto masu numfashi a girgizar kasar Morocco

An fara cire rai daga yiwuwar iya ceto masu sauran numfashi a baraguzan gine-ginen da girgizar kasa mai karfin maki 6.8 ta rusa a Morocco bayan da zuwa yanzu aka tabbatar da gano gawarwakin mutum dubu 2 da 900 baya ga wasu dubu 5 da 330 da suka jikkata.

Har a jiya laraba sai da aka yi nasarar ceto masu numfashi a baraguzan gine-ginen na Morocco.
Har a jiya laraba sai da aka yi nasarar ceto masu numfashi a baraguzan gine-ginen na Morocco. © REUTERS
Talla

Fiye da sa’o’I 80 bayan faruwar girgizar kasar ta tsakaddaren juma’ar da ta gabata har a safiyar yau alhamis jami’an agaji na ci gaba da aikin ture baraguzen gine-gine don ciro daruruwan mutanen da har zuwa yanzu ba a kai ga jin duriyarsu ba, musamman a kauyukan da ke kan tsaunuka, ko da ya ke an cire rai daga yiwuwar samun masu sauran numfashi.

Mahukuntan kasar ta Morocco na amfani da manyan motocin dakon kaya wajen aikin rabon kayakin abinci ga dubunnan mutanen da girgizar kasar ta raba da muhallansu kuma yanzu haka ke matsugunan wucin gadi cikin yanayi na tagayyara.

Girgizar kasar da ke matsayin mafi muni da Morocco ta gani a tarihi, majiyoyi sun bayyana cewa har zuwa yanzu abinci da tantunan tsugunar da jama’a shi ne abin da aka fi bukata sai kuma magunguna kula da wadanda ibtila’in ya jikkata.

Fahad Abdullah al Dosanri guda cikin jagororin jami’an kai daukin gaggawa na Qatar da ke aikin bayar da agaji a Morocco ya ce har a jiya laraba an yi nasarar ceto masu numfashi sai dai yanayin hanya ya hana su isa ga galibin yankunan kan tsaunuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.