Isa ga babban shafi

Har sai Somalia ta kawar da talauci za a iya murkushe Al-Shabab- Barre

Fraministan Somalia Hamza Abdi Barre ya alakanta tsananin yunwar da kasar ke fama da shi sakamakon fari da kuma rikicin siyasa baya ga rarrabuwar kan jama’a a matsayin manyan dalilan da suka hana gwamnatin kasar iya kammala kakkabe mayakan kungiyar al-Shabab cikin kusan shekaru 20 da ta shafe ta na yakarsu.

Firaministan Somalia Hamza Abdi Barre.
Firaministan Somalia Hamza Abdi Barre. via REUTERS - PRESIDENTIAL PRESS SERVICE
Talla

Dakarun Sojin Somalia da mayakan sa kai da ke fatan ganin kasar ta fice daga matsalolin mayakan ‘yan ta’adda sun shafe kusan shekaru 20 zuwa yanzu suna gwabza yaki da kungiyar ta al-Shabab ba tare da nasarar kawar da su ba.

Wannan yaki kuwa na gudana ne duk da tallafin kasashen duniya ga Somalia kama daga aiko da sojoji na musamman ko kuma taimakon kasar da kayan yaki.

Har zuwa yanzu al-Shabab ke da karfin iko a yankunan kudanci da kuma tsakiyar Somalia, batun da Framinista Abde Barre yayin zantawarsa da Aljazeera ke cewa dole sai an magance matsalolin kasar za a iya kawar da barazanar kungiyar.

A baya-bayan nan ne shugaba Hassan Sheikh Mohamud ya kaddamar da wani gangamin kammala murkushe kungiyar wanda ya ce da kansa zai jagoranci dakarun kasar, matakin da ke zuwa bayan kungiyar Tarayyar Afrika ta sanar da shirin janye dakarunta daga kasar.

Sai dai Fraministan na Somalia Hamza Abdi Barre ya ce babban aikin da ke gaban gwamnati a yanzu shi ne yaki da talauci da yunwar da ta addabi al’ummar kasar baya ga dakile bangarorin da ke yunkurin ballewa don neman ‘yancin cin gashin kansu, domin ta haka ne kadai za a iya ceto kasar ta Somalia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.