Isa ga babban shafi

Al'ummar Liberia na kada kuri'a a zaben shugaban kasa da 'yan majalisu

Al’ummar Liberia sun fita rumfunan zabe don kada kuri’a a zaben shugaban kasa da na ‘yan Majalisu, zaben da ‘yan takara 20 ke fafatawa, ciki har da shugaba mai ci George Weah wanda ke neman wa’adi na biyu a mulkin kasar.

Shugaba George Weah na neman wa'adi na biyu a mulkin kasar ta Liberia.
Shugaba George Weah na neman wa'adi na biyu a mulkin kasar ta Liberia. Reuters/Thierry Gouegnon
Talla

Tun da misalin karfe 8 na safiyar yau Talata aka bude runfunan zabe a sassan Liberia inda ake sa ran akalla 'yan kasar mutum miliyan 2 da dubu 400 su kada kuri’a a zaben wanda ‘yan takara 20 ke fafatawa ciki har da mata 2.

Duk da cewa George Weah mai shekaru 57 na da kwarin gwiwar samun nasara a zaben, amma ya na fuskantar gagarumin kalubale daga dan takarar babban jam’iyyar adawa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joseph Boakai mai shekaru 78.

Jigon adawa

Mr Boakai wanda ya yiwa gangamin yakin neman zabensa lakabi da ‘‘ ceto’’ ya caccaki salon mulkin Weah da cewa ya mayar da kasar baya cikin shekaru 6 da ya shafe ya na mulkar kasar.

Sai dai Weah na kafa hujja da yadda ya habaka bangaren ilimi da kuma kange kasar daga fadawa mashassharar tattalin arziki duk da kalubalen da duniya ke fama da shi na tsadar kayayyaki da tabarbarewar tattalin arziki.

Mr Weah, tsohon dan kwallo da ya lashe gwarzon shekara na FIFA a 1995, a shekarar 2017 ne ya tsunduma harkokin siyasa tare da lashe zaben kasar da rinjaye kashi 61 na yawan kuri’un da aka kada wanda ya bashi damar gadar shugaba Ellen Johnson Sirleaf da ke matsayin mace ta farko da ta hau kujerar shugabancin kasa a Afrika.

Wannan zaben dai shi ne karon farko da yaran da aka haifa ba a lokacin yaki ba, za su kada kuri’a, bayan yakin basasar da kasar ta gani shekaru 20 da suka gabata wanda ya kashe mutane akalla dubu 250.

Fargabatar tashin hankali

An dai yi fargabar samun tashe-tashen hukula, amma ga dukkan alamu zaben ya gudana cikin lumana, kamar yadda Lawali Mai Aiki mazaunin Monrobiya ya shaida mana.

Ku latsa alamar sauti, domin sauraran yadda zaben ya gaduna.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.