Isa ga babban shafi

Kotu ta amince da hukuncin daurin shekaru 20 akan kwamandan yan tawayen Liberia

Kotun daukaka kara a kasar Switzerland, ta amince da hukuncin daurin shekaru 20 da aka yankewa tsohon shugaban ‘yan tawayen Liberia, Alieu Kosiah, wanda aka tabbatar da cewar ya aikata laifuffukan yaki lokacin basasan da akayi a kasar su. 

Mayaka daga Ulimo, wadanda Alieu Kosiah ke jagoranta, an dauki wannan hoton ranar 27 ga watan Oktoba, 1992.
Mayaka daga Ulimo, wadanda Alieu Kosiah ke jagoranta, an dauki wannan hoton ranar 27 ga watan Oktoba, 1992. AFP - ALAIN BOMMENEL
Talla

Tun a watan Yunin shekarar 2021 kotun tarayya a Switzerland ta samu Kosiah da aikata laifuffukan yakin da akayi a Liberia tsakanin shekarar 1989 zuwa 2003 wanda yayi sanadiyar hallaka mutane sama da 250,000. 

Kotun dake birnin Bellinzona ta samu tsohon kwamandan da karya dokokin yaki na duniya, wanda shine hukunci irinsa na farko da aka yanke akan wani ‘dan kasar Liberia akan shari’ar da ta shafi laifuffukan yakin. 

Kosiah wanda ya koma zama a Switzerland a shekarar 1998 ya fada hannun jami’an tsaro ne a shekarar 2014 kafin ayi masa shari’ar wanda yace bai gamsu da hukuncin ba. 

Kotun daukaka karar ta kuma bukaci fitar da shi daga cikin kasar Switzerland da kuma hana shi shiga cikin ta na shekaru 10. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.