Isa ga babban shafi

Kotu ta yanke hukuncin kisa kan mutane 38 a Algeria

Kotu a Algeria, ta yanke wa mutane 38 hukuncin kisa a wannan Litinin, bayan samunsu da laifin yi wa wani mutum kisan gilla bisa zarginsa da tayar da wata gobarar daji, da ta yi sanadin mutuwar mutane kusan 100 a shekarar 2021.

Wasu jami'an kashe gobara a kusa da wata motar bas da wutar daji ta kone dauke da mutane 12 a kasar Algeria.
Wasu jami'an kashe gobara a kusa da wata motar bas da wutar daji ta kone dauke da mutane 12 a kasar Algeria. © AFP file photo
Talla

Baki dayan mutanen da aka yanke wa hukuncin za su yi zaman daurin rai da rai ne a gidan Yari, la’akari da cewar tun shekarar 1993 gwamnatin Algeria ta kawo karshen zartas da hukuncin kisa a kasar.

Mutane 94 ne dai suka gurfana gaban kotun ta Algeria bisa tuhumarsu da hannu a kisan gillar da aka yi wa Jameel Bin Isma’il mai sana’ar fenti a yankin Kabylie.

Bayan shafe watanni  ana zaman shari’ar, kotu ta sallami mutane 27, yayin da ta yanke hukuncin daurin shekarun da suka kama daga 3 zuwa 20 a kan ragowar 29.

Gabanin kisan da aka yi masa, Jameel ya mika kansa ne ga jami’an tsaro bayan da ya samu labarin zargin da ake masa na tayar da gobarar dajin da ta halaka mutane 90 a sassan Algeria.

Daga bisani ne kuma hotunan bidiyo suka yadu a kafofin sada zumunta, wadanda suke nuna yadda mutane suka yi wa motar ‘yan sandan da Jameel ke ciki kawanya, inda suka rufe shi da duka, tare da figo shi daga cikin motar, suka kuma cinna masa wuta, hakan bai isa ba, har sai da aka samu wasu masu daukar hotunan kasu a kusa da gawarsa bayan kone shi da suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.