Isa ga babban shafi
TATTALIN ARZIKI

Shugaban Malawi ya haramtawa kansa da jami'ansa tafiya kasashen ketare

MALAWI – Matsalar tattalin arziki ta tilastawa shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera haramtawa kansa tare da ministocinsa tafiya kasashen waje, yayin da ya bukaci jami’an da yanzu haka suka yi tafiya da su gaggauta komawa gida.

Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera
Shugaban kasar Malawi Lazarus Chakwera AFP/Archivos
Talla

Yayin jawabi ga jama’ar kasar ta kafar talabijin, Chakwera yace ya haramta duk wata tafiya zuwa kasashen ketare ga daukacin jami’an gwamnatin Malawi a kowanne mataki har zuwa karshen watan Maris na shekara mai zuwa.

Daukar wannan mataki ya biyo bayan amincewar da hukumar lamuni ta duniya ta yiwa bukatar bashin da Malawi ta gabatar mata na bai wa kasar rancen dala miliyan 175 domin tada komadar tattalin arzikin kasa.

Shugaban ya kuma bada umarnin rage kashi 50 na alawus din da ake bai wa manyan jami’an gwamnati domin sayen man fetur.

A farkon wannan mako, gwamnatin ta sanar da karya darajar kudin kasar da kashi 44, abinda ya bai wa IMF damar amincewa da bukatar rancen da kasar ke bukata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.