Isa ga babban shafi
ZABEN LIBERIA

Shugaba Weah na Liberia ya amince da shan kaye daga abokin hamayyarsa Boakai

Shugaban Liberia kuma tssohon gwarzon kafar duniya,   George Weah ya amince da sha kayeaa hannun abokin hamayyarsa,  Joseph Boakai bayan gwabzawa da suka yi a zaben shugaban kasar, wanda ya kai su har zagaye na biyu, yana mai cewa ‘’lokaci ya yi da zai fifita kishin kasa sama ga komai’’.

Shugaban Liberia mai barin gado, George Weah.
Shugaban Liberia mai barin gado, George Weah. © AFP
Talla

Sakamakon karshe na wannan zabe ya  nuna  cewa Boakai ne ya lashe kashi 51 na zaben shugaban kasar Liberia, kasar da ‘yantattun bayi daaga Amurka suka kafa.

A jawabin da ya gabatar ga al’ummar kasarsa  a daren Juma’a, Weah ya ce,  ‘’sakamakon zabe ya nuna cewa  Boakai yana kan gaba, kuma babu yadda za aa yi mu kaamo shi’’

Waeh y ace jam’iyyyarsa ta CDC taa fadi zabe, amma Liberia ta yi nasara, kuma yanzu ne lokacin da za a nuna sanin yakamata a duk kuwa  da rashin nasara.

Boakai, mai shekaru 78 ya yi rashin nasara a haannun Weah mai shekaru 57  a zagaye na biyu naa zaben sekarar 2017 da tazara  mai yawa.

A  wannan zaben da aka yi, Boakai ya bai wa Weah rata da kuri’u dubu  28, kaamar yadda sakamakon na Juma’aa ya nuna.

Zaben Weah, wanda shine dan Afrika na farko da ya  lashe kyautar kwallon kafa ta duniya  da hukumar kwallon kafar FIFA ke bayarwa ya bada kwarin gwiwar  lalubo canji  a Liberia, wadda ke farfadowa daga tasirin yakin basasa da na annobar Ebola a shekarun 2014 daa 2016.

Amma masu lura da al’amura su caccaki gwamnatinsa, su na mai zarginta da rashawa, da kuma gazawa wajen cika alkawurrran da ta  daukar wa al’umma.

 

Shugabannin kasashe sun fara aikewa da sakwannin taya murna ga zababben shugaban Liberia Joseph Boakai, cikin su har da shugaba Joe Biden na Amurka da Bola Ahmed Tinubu na Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.