Isa ga babban shafi

Kungiyoyin fararen hula sun bukaci ECOWAS ta haramta yin wa'adi na 3

Afirka – Cibiyar bunkasa dimokiradiya ta Afirka da ake kira CDD tare da wasu kungiyoyin fararen hula a yankin, sun bukaci kungiyar ECOWAS da ta amince da wani daftari wanda zai shata wa'adin mulkin da kowacce kasa za tayi amfani da shi a yankin domin tabbatar da dimokiradiya.

Tutar kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS/CEDEAO
Tutar kungiyar kasashen yankin yammacin Afirka ta ECOWAS/CEDEAO REUTERS - FRANCIS KOKOROKO
Talla

Wadannan kungiyoyi sun ce yin haka zai hana wasu shugabannin dake yankin amfani da karfin mulki wajen sauya kundin tsarin mulkinsu domin ci gaba da zama a kan karaga, bayan kammala wa'adinsu guda 2.

Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara na daya daga cikin wadanda suka sauya kundin tsarin mulkin kasarsu
Shugaban Cote d'Ivoire Alassane Ouattara na daya daga cikin wadanda suka sauya kundin tsarin mulkin kasarsu REUTERS - FRANCIS KOKOROKO

Wannan sanarwar na zuwa ne a daidai lokacin da shugabannin kasashen ECOWAS dake cikin kungiyar ke shirin gudanar da taron su gobe lahadi, domin nazari a kan halin da ake ciki a Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso da Mali da kuma Guinea, wadanda sojoji suka karbe mulkinsu daga zababbun shugabanni.

Ana kuma saran shugabannin su duba yunkurin juyin mulkin da aka yi a Saliyo da Guinea Bissau a makwannin da suka gabata.

Wadannan kungiyoyi sun ce gabatar da wannan bukata ya zama wajibi domin bunkasa harkokin dimokiradiya a yankin dake fama da tashe tashen hankula da kuma shugabannin da basa son sauka a karagar mulki.

Yadda aka yi ta zanga zanga bayan shugaba Alpha Conde na Guinea ya sauya kundin tsarin mulkin kasarsa
Yadda aka yi ta zanga zanga bayan shugaba Alpha Conde na Guinea ya sauya kundin tsarin mulkin kasarsa AFP - CELLOU BINANI

Daya daga cikin masu shirya taron, Paul Osei-Kuffour yace kashi 75 na mutanen da suka fito daga kasashe 34 dake Afirka na bukatar ganin an gindaya sharadin wa'adin da kowanne shugaba zai yi, ba tare da bashi damar sauya kundin kasar sa ba.

Osei-Kuffour yace zasu ci gaba da janyo hankalin bangarori da dama na kungiyoyin bunkasa dimokirdaiya, domin ci gaba da matsin lamba ga shugabannin domin amincewa da wannan shawara da kuma haramta yin wa'adi na 3 ga kowanne shugaban kasa.

Daraktan tsare tsare na kungiyar CDD a Ghana, Kojo Asante yace suna nazari a kan koma bayan da dimokiradiya ta samu a cikin shekaru 10 da kuma dalilan da suka sanya aiwatar da juyin mulki a wasu kasashe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.