Isa ga babban shafi

An cafke mutanen da ake tuhuma da kashe fitaccen dan tseren gudun Uganda

Rundunar ‘yan sandan Kenya ta kame wasu mutune biyu da ake tuhuma da hannu a kisan fitaccen dan tseren gudun kasar Uganda Benjamin Kiplagat, wanda aka gano gawarsa cikin mota dauke da raunukan da ke nuna daddaba masa wuka aka yi a ranar lahadin da ta gabata.

Fitaccen dan tseren gudun kasar Uganda Benjamin Kiplagat da 'yan fashi suka kashe a Kenya.
Fitaccen dan tseren gudun kasar Uganda Benjamin Kiplagat da 'yan fashi suka kashe a Kenya. AFP - FABRICE COFFRINI
Talla

Karamin kwamandan ‘yan sanda Stephen Okal, ya shaidawa manema labarai cewa, an samu wukar da aka yi amfani da ita wajen kashe Kiplagat mai shekaru 34 a hannun daya daga cikin mutanen da aka cafke.

Jami’in tsaron ya ce bincikensu ya nuna cewar an kashe fitaccen dan tseren gudun ne a lokacin da aka yi kokarin yi masa fashi, la’akari da cewar makasan sun sace wayarsa ta hannu da kuma kudaden da ke jikinsa.

An gano gawar Kiplagat a wajen Eldoret, birni na biyu mafi girma a Kenya, inda manyan masu wasannin motsa jiki kamar na tseren gudu ke zuwa domin yin atasaye, kasancewar garin na kan tudu.

Bincike ya nuna cewar Kiplagat ne fitaccen dan wasan tseren gudu na hudu da aka kashe a yankin na Eldoret, bayan takwarorinsa da suka hada da Agnes Tirop da Damaris Muthee da kuma Rubayita Siragi ‘yar kasar Rwanda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.